Site icon Muryar 'Yanci

Babu Gaskiya A Labarin CORONA Ta Kama Alkalin Alkalai – Kotun Koli

Daraktan yada labarai na babbar Kotun koli, Dr Festus Akande, ya ce rahoton da ake ya?awa a wasu kafafen watsa labarai cewa Al?alin Alkalan Najeriya, Tanko Mohammed, ya kamu da Korona ba gaskiya bane jita-jita ne kawai, da wasu suka ?irkiro domin cimma wata manufa kawai.

Akande ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar bayan wani Alkalin kotuna koli, Ibrahim Saulawa, ya bayyana a wani taro a Abuja cewa Alkalin Alkalan ya kamu da Korona kuma an fitar da shi waje.

Tun a ranar Talata, mai magana da yawun Alkalin Alkalan ya karyata rahoton cewa mai gidansa na rashin lafiya. Ana kyautata zaton ya fitar da wannan jawabi na biyu ne domin martani ga Alkali Ibrahim Saulawa.

Akande yace: “Biyo bayan an fitar da jawabin farko ina sake jaddada cewa babu wani rahoton asibiti dake nuna Alkalin alkalai ya kamu da cutar Coronavirus.”
“Masu yada jita-jita su kara bincike kuma su samo takardar gwajin asibiti da aka dogara da shi.”

A halin yanzu babban alkalin yana Dubai, daular larabawa inda yake samun kular kwararrun masana kiwon lafiya. Daya daga cikin alkalan kotun koli, Mai shari’a Ibrahim Saulawa ya bayyana hakan yayin kaddamar da hedkwatar kungiyar lauyoyi musulmai a ranar Talata a garin Abuja.

Exit mobile version