Babban zauren Majalisar ?inkin Duniya ya kada kuri’ar dakatar da Rasha daga hukumar da ke kare hakkin dan Adam yayin wani zama da aka yi a birnin New York.
Matakin ya biyo bayan tuhumar da ake ma Rasha cewa sojojinta na aikata laifukan yaki a Ukraine.
Kafin a akada kuri’a, jakadan Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya SErgiy Kyslytsya ya tuhumi Rasha da aikata munanan laifuka – musamman bayan kashe-kashen da ake tuhumar Rashar da aikatawa a garin BUcha.
Wakilin Rasha Gennady Kuzmin ya yi tir da kuri’ar, sannan kuma wasu kasashe, ciki har da Koriya ta Arewa da Syria sun mara ma sa baya.

