Daga Waje Ne Aka Dauki Nauyin Shirya Zanga-Zangar Najeriya – Kashim Shettima

Kashim Shettima office portrait

Yayin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki da ke kara fusata jama’a kan Gwamnatin shugaba Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya zargi ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da cewa su ne ke da hannu wajen shirya zanga-zangar da za a yi a watan Agusta a fadin kasar, inda ya kira su ‘yan iska. Da yake jawabi a wajen wani daurin aure a Maiduguri, jihar Borno a ranar Asabar, Mista Shettima ya bayyana wadanda suka shirya zanga-zangar na watan Agusta a matsayin ‘yan fashi da wawaye a ?asashen…

Read More

Kotun Koli Ta Sanar Da Ranar Ritayar Alkalin Alkalai

IMG 20240730 WA0189

Kotun koli ta sanar da cewa Olukayode Ariwoola zai yi ritaya a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya a ranar 22 ga watan Agusta. A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Festus Akande mai magana da yawun kotun koli ya ce za a gudanar da zaman kotun na ban kwana domin girmamawa ga alkalin alkalan wanda ke cika shekaru 70 na ritaya. Akande ya kuma ce kotun kolin ta fara hutun ta na shekara a ranar 22 ga watan Yuli inda za ta dawo a ranar 23 ga watan Satumba…

Read More

Zanga-Zanga: Ba Za Mu Amince A Kifar Da Gwamnatin Tinubu Ba – Shugabannin APC

images 2024 03 06T195109.222

Shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 da Abuja sun ci alwashin cewa ba za su zuba ido su na kallo wasu batagari su kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba da sunan zanga-zanga. Sakataren kungiyar ciyamonin APC na ?asa, wanda kuma shine Ciyaman din jam’iyyar a Cross River, Alphonsus Ogar Eba a taron manema labarai a shelkwatar jam’iyyar ta ?asa a yau Litinin ya ce zanga-zangar ta kwanaki goma wani shiri ne na kifar da gwamnatin Tinubu. Ciyamonin jam’iyyar sun yi garga?in cewa duk wanda ya gaje da zanga-zangar…

Read More

Babu Dalilin Zanga-Zanga, Mun Magance Da Yawa Daga Cikin Bukatun Masu Zanga-Zangar – Fadar Shugaban Kasa

IMG 20240225 WA0030

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu babu bukatar yin zanga-zanga domin tuni ta fara tinkarar bukatun ‘yan Najeriya da ke ci gaba da kokawa. Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Yau Litinin Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, “Ana magance da yawa daga cikin batutuwan da masu shirya zanga-zangar suke tadawa, gwamnati na kokarin ganin an samar da abinci. .” “An raba shinkafar zuwa cibiyoyi daban-daban a fadin kasar nan, ana kuma sayar da…

Read More