Alaramma Ismail Maiduguri ya zargi wasu daga cikin malaman musulunci da kiristanci da biyewa ‘yan siyasa lokacin zabe Malamin Al-Kur’anin ya ce yawan cikan sahu a masallatai da coci ake amfani da su a wajen sayen bakin malamai Gwani Ismail Maiduguri ya ce tun da an karbi kudin ‘yan siyasa, dole yanzu ba za a iya kokawa da irin mulkinsu ba Ismail Maiduguri ya tofa albarkacin bakinsa game da halin da Najeriya take ciki a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu. Alhafiz Ismail Maiduguri ya ce a yanzu ‘yan siyasa sun…
Read MoreDay: May 12, 2024
Ba Za Mu Amince Da Harajin Internet Ba Har Sai An Samar Wa ‘Yan Najeriya Hanyoyin Samu – Sanata Ndume
Sanata Ali Ndume ya soki harajin yanar gizo da babban bankin Najeriya ya bullo da shi kwanan nan, inda ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da dorawa ‘yan Najeriya haraji ba tare da kara musu kudaden shiga ba. Dan majalisar Dattawa na jam’iyyar All Progressives Congress mai wakiltar mazabar Borno ta kudu ya bayyana haka a shirin Siyasar Yau na Channels Television a Jiya Juma’a. Ndume ya jaddada cewa harajin da aka saka ta yanar gizo zai kara dora wa ‘yan Najeriya nauyi, Yana mai…
Read MoreLASSA: Mutum 857 Sun Kamu Yayin Da Ta Hallaka Mutum 156 A Bana – NCDC
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa Zazzabin Lassa ta yi ajalin mutum 156 sannan mutum 857 sun kamuwa da ita daga Janairu zuwa ranar 28 ga Afrilu 2024. Hukumar ta ce alkaluman yaduwar cutar ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ta kashe a wannan lokaci ya zarce yawan mutanen da cutar ta kashe a irin wannan lokacin shekarar 2023. NCDC ta ce an samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar daga mutum 11 a mako 16 zuwa mutum 14 a mako 17.…
Read MoreTinubu Ya Umarci Babban Banki Ya Dakatar Da Shirin Harajin Internet
Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu bayan dawowarsa daga godon tafiya ya tarar da wani umarnin Babban Bankin Najeriya na CBN na shirin karawa Yan Najeriya ku?i, kaso 0.5 Sai dai Shugaban Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa tuni ya tura umarni akan Babban Bankin Najeriya CBN ya sauka daga kan wannan ku?iri na karawa yan Najeriya haraji a bankuna don samar da tsaron yanar gizo.. Tinubu ya bayyana cewa, wannan tsari na babban Bankin kasa bai da ce da wannan lokacin ba, saboda halin da Yan kasa ke ciki a…
Read MoreAsusun Bada Lamuni Na Duniya (IMF) Ya Soki Lamirin Tinubu Na Dawo Da Tallafin Mai A Boye
Asusun ba da lamuni da duniya (IMF) ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye. Hukumar ta ce dawo da tallafin da aka yi a boye zai cinye kusan rabin kudin shiga da kasar za ta samu daga arzikin man fetur. Asarar da Najeriya za ta yi IMF ta ce matakin zai la?ume akalla N8.43trn daga cikin N17.7 trn da ake sa ran samu daga cire tallafin man fetur. Wannan na kunshe ne a cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar kan Najeriya…
Read More