Rahotanni daga kasar Amurka na bayyana cewar Gwamna Andrew Cuomo na jihar New York ta kasar ya yi murabus daga mukaminsa bisa zargin da ake masa na neman mata, ba bisa ka’ida ba.
Gwamnan ya sha matsin lamba daga mutane da dama na ya sauka da matsayin gwamna bayan wasu mata da dama sun zarge shi da cin zarafinsu.
Ya sanar da matakin murabus ?insa ne biyo bayan wani rahoto da ofishin Antoni Janar na jihar ya nuna zarginsa da cin zarafin mata a lokuta da dama.
Gwamna Cuomo ya fa?a ranar Talata cewa: “Duba da halin da ake ciki, Matakin da ya fi dacewa na dauka wanda zan taimaka shi ne na sauka na bar gwamnati ta cigaba da aikinta.
“Saboda haka na sauka daga matsayin gwamna saboda ku nake wa aiki, kuma aiki mai kyau shine in kyautata muku.” Gwamnan ya ala?anta lamarin da COVID19.
A cikin jawabinsa gwamnan ya yi tsokaci kan halin da ake ciki na korona ga kuma zargin da ake masa, yace: “Muna cikin wani yanayi na rayuwa ko mutuwa.
Ga ayyukan gwamnati kuma ga wasu abubuwa na shagala, wannan shine kololuwar abinda ya kamata gwamnati ta yi. Kuma banason zama sanadin gazawar gwamnati.”
“Ina kaunar New York kuma ina kaunar mutanen New York, wannan soyayyar da nake wa jihar mu ita ke karamun karfin guiwa a kan duk abinda na yi. Saboda haka bana son in zama mutum mai son kansa.”

