Site icon Muryar 'Yanci

Zanga-Zangar Lekki: Da Harsashin Roba Soji Suka Yi Amfani – Kuka-She?a

Tsohon Kakakin rundunar Sojin Najeriya Birgediya Sani Usman Kukasheka mai ritaya, ya ce sojoji sun harba harsashin roba ne, ba na gaske ba, a kan dandazon masu zanga-zanga da suka mamaye yankin Lekki a garin Legas.

Kafafen yada labarai da dama, a gida da ketare, sun wallafa rahotannin cewa sojojin Najeriya sun budewa fararen hula masu zanga-zanga wuta a Lekki.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin tare da kafa kwamitin bincike da zai bankado gaskiyar abinda ya faru a Lekki.

Da ya ke magana a wani shirin gidan Talabijin din ‘Arise’ a ranar Alhamis, Usman Kukasheka ya ce harsashin roba ba ya kisa, a saboda haka babu gaskiya a rahotannin da ke cewa an rasa rayuka a Lekki.

Yayin tattaunawar da aka yi da shi, Kukasheka ya ce akwai dalilai masu karfi da suka tilasta gwamnati yin amfani da sojoji a kan masu zanga-zanga.

A cewarsa, wasu kungiyoyi na gida da ketare sun fara saka jari a zanga-zangar, lamarin da ya haddasa barkewar rikici a sassan Najeriya, wanda kuma hakan ne yasa gwamnati yin amfani da sojoji.

“Tabbas, an tura sojoji, amma kwamitin bincike zai gano silar dalilin tura sojoji da abin da ya faru bayan isarsu wurin.
“Za mu bar kwamitin bincike ya yi aikinsa, amma jama’a su sani cewa sojoji sun harba harsashin roba ne, wanda ba ya kisa koda kuwa an harbi mutum a kusa ne.

“Akwai matukar hatsari jama’a suke saka siyasa a batun tsaron kasa. Bai kamata a yi kokarin kawo siyasa da raba kan rundunar soji ba,” a cewar Kukasheka.
Masu zanga-zangar EndSARs sun zarce da kashe-kashe tare da kone-kone wanda ya koma tarzoma.

Exit mobile version