Iyalan Shugaba Buhari da na mataimakinsa Osinbajo sunbi sahun masu zanga-zanga
Zahra Buhari da Kiki Osinbajo sunbi sahun masu zanga-zanga kawo karshen zaluncin jami’an SARS.
Iyalan Shugaban Najeriya da na mataimakinsa wato Zahra Buhari da Kiki Osinbajo, sun shiga zanga-zangar kawo ?arshen azabtarwar da ake zargin yan sandan SARS ke yi a Najeriya.
Yar gidan Shugaba Buhari, wato Zahra, ta wallafa wani hoto a shafinta na Instagram, wanda masu gudanar da irin wannan zanga-zanga musamman a shafukan sada zumunta suke wallafawa na kawo ?arshen azabtarwar.
Ita kuwa yar gidan Osinbajo, ta yi amfani da duka mauduan guda biyu, wato na #endpolicebrutality da kuma na #endsars, maana tana goyon bayan kawo ?arshen azabtarwar da yan sanda ke yi da kuma soke rundunar SARS.

