Site icon Muryar 'Yanci

Zanga-zanga Ta Yi Rana: An Soke Rundunar SARS A Najeriya

Bayan lashe kwanaki da wasu ‘yan Najeriya suka yi suna gudanar da Zanga-zangar neman a soke rundunar SARS mai ya?i da manyan laifuka, daga bisani ha?arsu ta cimma ruwa inda Gwamnatin tarayya ta amince da soke rundunar.

Babban Shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke ya?i da fashi da makami a Najeriya wato SARS.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai tsaye ga manema labarai a ranar Lahadi.

Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ?auki kwanaki ana yi a wasu jihohin ?asar, inda ko a yau ma sai da aka yi irin wannan zanga-zangar a Ingila.

‘Yan ?asar dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ?a’ida ba da sa?a dokokin aiki.

A baya dai gwamnatin ?asar ta ce ba za ta soke rundunar ba, sai dai ta yi mata sauyi ko kuma kwaskwarima kan yadda rundunar ta ke gudanar da ayyukanta, inda ko a kwanakin baya sai da Shugaban Majalisar Dattawan ?asar Ahmed Lawan ya ce ba zai yiwu a soke rundunar ba sai dai a sauya tsarinta.

Hakazalika wasu daga cikin ?usoshin gwamnatin ?asar da wasu gwamnoni da mu?arraban shugaban ?asar na da irin wannan ra’ayi.

Exit mobile version