Site icon Muryar 'Yanci

Zan Yi Kewar Fadar Shugaban Kasa – Aisha Buhari

Uwar gidan shugaban kasa mai barin gado, Aisha Muhammadu Buhari ta ce abin da za ta fi kewa a fadar shugaban ?asa shi ne yawon da take yi da daddare, inda ta ce ta kan yi tattaki daga ofishin shugaban ?asa zuwa kofar shiga fadar.

A hirarta ta musamman da BBC a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja, Hajiya Aisha Buhari ta ce kuma ya kamata a bai wa matan tsofaffin shugaban ?asa alawus-alawus saboda irin nauyin da yake rataye a kansu, inda ta ce zai yi kyau a ri?a basu kamar yadda ake bai wa mazajensu.

Mai ?akin shugaban Najeriyar ta ce za ta bi mijinta zuwa Daura har tsawon lokacin da zai zauna a can bayan sauka daga mulki ba wai komawa Dubai ba kamar yadda wasu ke ra?e-ra?e a fa?in ?asar.

Ta ce abin da za ta mayar da hankali da zarar sun mi?a mulki shi ne kula da yaranta da kuma jikokinta saboda “shekara takwas da suka wuce ban samu lokacin yin hakan ba saboda mulki,” in ji Aisha.

Hajiya Aisha Buhari ta ce ya kamata a bai wa matan tsofaffin shugaban ?asa alawus-alawus saboda irin nauyin da yake rataye a kansu

Ta ce akwai yiwuwar za ta sake bu?e makarantarta ta koyawa mutane sana’o’in hannu wanda take da lasisinsa tun kafin su hau mulki.

Exit mobile version