Site icon Muryar 'Yanci

Zan Sadaukar Da Kujerata Domin Zaman Lafiyar Katsina – Sarkin Katsina


Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya bayyana cewar zai iya sadaukar da kujerar shi, idan har hakan zai sanya a samu zaman lafiya a Jahar Katsina.

Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi, a taron tsaro da ya shirya domin gano hanyoyin da za’a samar da dauwammen zaman lafiya a jahar Katsina.

Taron wanda ya gudana a ?akin taro na Hukumar kula da ma’aikatan ?ananan Hukumomi ta Jahar Katsina, ya samu halartar Hakimai, Al?alai, da Lauyoyi, da Limamai, da Jami’an tsaro da ?an Bijilante, da Maiba Gwamna Shawara na Musamman akan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina da sauran su.

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman
yace an shirya taron ne domin tattaunawa akan matsalolin tsaro dake cigaba da ?aruwa a jahar, tare da gano hanyoyin da za’a magance su a Jahar Katsina.

Uban ?asar ya bayyana damuwa na yanda wasu Al?alai, da Lauyoyi, da ?an ?ungiyar kare ha??in ?an adam suke kare ?an ta’adda a Kotu, sai ya bu?ace su da suji tsoron Allah a dukkanin abinda suke yi na rayuwa.

Mai Martaba Sarkin ya umarci Hakimai da su kafa wani asusu
daza’a bada tallafi domin amfani dasu, wajen inganta tsaro a yankunan su, inda yace masarautar tuni ta fara haka, kuma an samu ku?a?e masu yawa da a halin yanzu za’ayi amfani dasu wajen tsaro.ADVERTISEMENT

Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya nanata bu?atar dake akwai na ?aukar matakin gaggawa ga ?an bindiga da?i, da masu fya?e da sauran ?an ta’adda, wanda acewar sa hakan zai samar da tsaro a jaha dama ?asa baki ?aya.

Maiba Gwamna Shawara na Musamman akan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina yayi jawabi akan ?umbin nasarorin da aka cimmawa, biyo bayan dokar tabbatar da tsaro da gwamnatin Jahar ta sanya.

Alhaji Ibrahim Katsina yace Gwamnatin Jahar ta ?auki ?an ?ungiyar Bijilante guda 3000 domin marawa jami’an tsaro baya wajen samar da tsaro a jahar.

Kwamishinan ?an sanda na Jahar CP Sanusi Buba wanda ya samu wakilcin Mai magana da yawun Rundunar ?an Sandan Jahar SP Gambo Isah, ya ?u?aci Al’umma dasu cigaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya da ha?in kai domin samar da tsaro a Jahar.

Exit mobile version