Site icon Muryar 'Yanci

Zan Nemi Kujerar Gwamnan Kaduna A 2023 – Isa Ashiru Kudan

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Hon Isa Kudan Ashiru ya ce shi ya samu nasara a zaben 2019 amma magudi aka tafka masa, amma zai kara tsayawa takarar a shekarar 2023.

?an siyasar ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna, ya kara da cewa yana siyasa ne don yi wa mutane aiki sannan ya shayar da jama’arsa romon dimokradiyya.

Kudan ya ce babu shakka zai kara tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar PDP kuma a cewarsa babu gudu babu ja da baya. Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare Kamar yadda dan takarar ya ce: “Ina da burin jajircewa a kan wannan kudirin nawa har sai na samu nasara.”

Idan ba a manta ba Ashiru ya rike kujerar dan majalisar tarayyar jihar Kaduna har sau biyu sannan ya dare kujerar dan majalisar wakilai shima har sau biyu. Ya tsaya takara tare da Gwamna Nasir El-Rufai a karkashin jam’iyyar APC a 2015 sai dai tun a zaben fitar da gwani ya sha kaye wanda daga nan ya koma jam’iyyar PDP kafin zaben 2019.

Exit mobile version