Site icon Muryar 'Yanci

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Mi?a Makamai

A cigaba da yunkurinta na tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin Al’ummar Jihar Zamfara, Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, a yau ta yi ta yi nasarar karbar tubabbun yan bindiga Shida.

Tubabbun yan Bindigar da ka aika-aika a dajin dunburun na kamar hukumar Zurmi karkashin jagorancin Auwallun Daudawa, sun mika bindigogi 22 tare da albarussai. A yayin karbar bindigogin gwamnatin Jihar Zamfara ta gayyato majalissar malamai ta Jihar wadanda su ka yi masu wa’azi akan muhimmancin zaman lafiya da kuma amfanin sulhu daga nan imam Malam Abubakar Fari, ya rantsar da su da alkur’ani mai girma akan ba za su kara fashin daji, shaye-shaye, taimakawa masu aika-aika da duk wani aikin assha mai kama da haka, ba.

Da ya ke jawabi mai daraja gwamnan Jihar Zamfara Hon Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun. Ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan tuba da wadannan mutane suka yi. Daga nan ya yi kira ga sauran takwarorinsu da ke cikin dazukkan Jihar Zamfara, da su yi koyi da wadannan domin samun zaman lafiya a Jihar da ma kasa baki daya. Haka zalika Gwamnan ya Kara nanata matsayar gwamnatinsa na cigaba da karbar wadanda su ka yarda za su yi sulhun. Tare da yakar wadanda su ka ki mika wuya.

Rantsar da tsofaffin Yan Bindigar dai ya s0amu halar, dukkanin shuwagabannin rundunonin tsaro na Jihar Zamfara, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Lawal Hassan Dan’iyan Anka, Hon. Mukthar Anka, Sakataren gwamnatin Jihar Zamfara Hon. Bala Bello Maru, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alh. Ibrahim Bello Gusau, Shugaban Ma’aikatan Zamfara. Hon. Kabir Balarabe Sardaunan Dan’isa, Shugwnan Jam’iyar PDP Alh. Tukur Umar Danfulani Gusau, Kwamishinoni, masu baiwa Gwamna shawara Malaman Addini da sauran muhimman mutane.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
SSA NEW MEDIA
8-2-2021

Exit mobile version