Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewar yan taadda masu Garukwa da mutane sun shiga garin Kanoma dake karamar hukumar Maru ta jahar Zamfara a jiya jumaa dai dai lokacin da ake gabatar da sallar jumaa suka tafi da mutane 30 cikin har da Limamin garin na Kanoma.
Lamarin satar jamaa a yankin Arewacin Najeriya na ?ara ?aukar sabon salo, inda a kusan kullum yan Bindiga ke kai farmaki akan jamaa su kashe na kashewa su kama na kamawa sannan su nemi ku?a?en fansa.
Gwamnatocin Jihohin Zamfara da Katsina inda Balain yan Bindigar ya fi tuazzara sun ?auki matakai a baya na yin sulhu da yan Bindiga amma bu?ata ba ta biya ba, maimakon biyan bu?ata sai abubuwa suka ?ara dagulewa.
Hakika akwai tashin hankali ace irin taron ranar jumaa dan taadda ya ratsa masallacin jumaa ya tafi da Limami da sauran jamaa.
Allah ya kawo mana karshen wannan balai.

