Site icon Muryar 'Yanci

Zamfara: Kalaman Mataimakin Gwamna Gaban Malaman Addini Sun Bar Baya Da Kura

Daga Ibrahim Madugu

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar an shiga rudani biyo bayan wasu kalaman da suka fito daga bakin sabon Mataimakin Gwamnan Zamfara Alh. Hassan Nasiha, a lokacin da Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta jihar Zamfara ta kai masa ziyarar taya murnar samun matsayin Mataimakin Gwamna ranar Alhamis, 10 ga watan Maris, 2022.

Da yake mayar da jawabi ga Malaman Addinin, Alh. Hassan Nasiha ya ce “A SHEKARAR 2011 IMANI NE YASA SUKA FA?I ZA?E” amma a cewar sa “YANZU BABU WANDA YA ISA YA KAR?I MULKI A HANUN SU A 2023”

Wadannan kalaman da mataimakin Gwamnan ya yi ga Malaman na addini sun harzuka musamman matasa daga cikin Malaman wa?an da shugaban su Sheikh Abubakar Fari ya jagoranta har sai da maganar ta fito aka ji ta.

“A cikin maganar akwai abin ?yama da damuwa sosai musamman ganin cewa a lokacin ziyarar Malaman addinin Musulunci ne Alh. Hassan Nasiha ya za?i ya yi ita wannan maganar mai zafi”.

Kamar yanda wani daga cikin Malaman ya fa?a, ina ma ace Mataimakin Gwamnan ya jira sai da wata ?ungiyar MAGUZAWA ta kawo masa ziyara sannan ya yi irin wannan kalaman.

“Fa?in wannan maganar a ziyarar Malamai masu ta?ama da koyarwar Annabi (SAW) da fa?akarwa a kan cewa Allah ke ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so kuma ta yadda ya so abin takaici ne da bakin ciki kuma ga dukkan musulmi.

“Hakazalika wannan maganar ta Mataimakin Gwamna ta nuna cewa gwamnatin ta su ta shirya yin aika-aika da ta’addanci da RASHIN IMANI kan bayin Allah domin su ci gaba da dorewa kan karagar mulkin da sun tabbatar da cewa ingantaccen za?e bazai basu dama ba”.

“Wani abin ba?in ciki shi ne ace wa?annan kalamai sun fito daga bakin jigon gwamnatin da ke i?irarin shari’ar musulunci da kare musulmi. Hakan yasa muke ji kamar an da?a ma Zamfarawa da al’ummar musulmi wu?a a ciki”.

“Muna fatan Malaman jihar Zamfara wa?anda ke cikin wannan tafiyar da wa?anda aka wakilta za su ?auki hannu daga maganar su tashi tsaye su sauke nauyin da Allah Ya aza masu na shiryarwa ta hanyar kira ga Mataimakin Gwamnan da ita kanta Gwamnatin da yake wakilta da ta yi gaggawar janye wannnan mugun kalami su kuma tubar ma Allah (SWA)”

“Haka ma muna amfani da wannan dama mu yi kira ga hukumomin tsaro da jama’ar jihar zamfara musamman samari da su rike Gwamnati akan jinin duk wani dan Siyasa ko Malami da ya rasa rayuwar shi, dukiyar shi ko lafiyar shi daga nan har zuwa lokacin jefa ?uri’a”.

Exit mobile version