Site icon Muryar 'Yanci

Zamfara: An Wanke ‘Yan Majalisar Da Aka Zarga Da Alaka Da ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Majalisar dokokin jihar ta ?auki matakin dawo da mambobinta guda biyu da ta dakatar a baya bisa zargin ala?a da yan bindiga.

Majalisar ta ?auki wannan matakin ne bayan amince wa da rahoton kwamitin ?a’a, wanda ya gudanar da bincike a kai. Yan majalisun biyu, Ibrahim Tudu-Tukur (Bakura) da Yusuf Anka (Anka) an dakatar da su ne a watan Oktoba bisa zargin suna da ala?a da yan bindiga a yankunan da suke wakilta.

?an majalisa Yusuf Kanoma, shi ne ya gabatar da kudiri kan dakatar da abokan aikinsa, inda ya yi zargin cewa Bakura da Anka, “Sun yi farin ciki da sace mahaifin kakakin majalisa, Marigayi Alhaji Mu’azu Magarya.”

Amma yan majalisun biyu sun musanta wannan zargi, kuma daga baya suka ce dakatar da su yana da ala?a da dambarwar siyasa.

A zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban kwamitin ?a’a, Kabiru Dansadau, ya gabatar da rahoton bincike kan zargin. Kwamitin a cikin rahotonsa ya wanke mambobin majalisan biyu daga zargin da ake musu na hannu a ayyukan yan bindiga a yankunan su.

Wani mamba a majalisar daga yammacin Zamfara, wanda ya nemi mu boye sunansa, ya bayyana cewa an dawo da mutanen biyu sabida, “Babu wata hujja da ta tabbatar da abinda ake zarginsu.” Hakanan kuma ya shaida wa manema labarai cewa wasu daga cikin dattawan Zamfara sun sa baki kan lamarin, shiyasa aka dawo da su.

Hadimin kakakin majalisar dokokin jihar, Mustapha Jafaru, ya tabbatar da cewa majalisa ta umarci su dawo bakin aiki amma ya musanta cewa wasu daga waje sun saka baki.

Exit mobile version