Site icon Muryar 'Yanci

Zaben Shugaban Kasa: Buhari Ya Kalubalanci Gwamnoni

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Buhari ya umarci dukkan gwamnonin jihohin ?asar na APC da su tabbatar da cewa sun nuna kyawawan ?abi’u da manufofin jam’iyyar a lokacin za?en fitar da gwani na shugaban ?asa.

Shugaban ?asar ya fa?i hakan ne a yayin wata ganawa da ya yi da gwamnonin 22, da kuma shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu a fadar shugaban kasa Abuja.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan ya?a labarai Femi Adesina ya fitar bayan ganawar, Buhari ya yi magana ne a kan muhimman abubuwa biyar.

Shugaban ya yi magana a kan za?ukan da ke tafe na 2023 da kuma nuna muhimmancin ha?in kan ?a?an jam’iyyar APC a wannan lokaci na za?ukan fitar da gwani.

Tsare-tsaren za?ukan 2023 sun kankama gadan-gadan, kuma na fahimci cewa jam’iyyun siyasar da suka fi nasara a fa?in duniya a ko yaushe suna dogara ne kan ha?in kan cikin gida da shugabanci na gari don samun manyan nasarori.

“Jam’iyyarmu ta APC ba za ta bambanta da sauran da suka yi nasara ba, har yanzu muna cigaba da aiwatar da tsare-tsaren samar da ?asa mai albarka”

“A yayin da na shiga shekarata ta ?arshe a karo na biyu a matsayin shugaban ?asa, na fahimci muhimmancin bu?atar da ke akwai ta na samar da shugabanci mai ?arfi a ?ar?ashin wannan sauyin mulkin, don tabbatar da cewa an yi komai cikin tsari, irin wannan shugabanci shi ake bu?ata don jam’iyyar ta cigaba da zama mai ?arfi kuma dun?ulalliya.

“Sannan shi ake bu?ata don bun?asa ribar dimokra?iyya wajen tabbatar da cewa jam’iyyar ta ci gaba da samun iko da ?asar, da samun yawan ‘?an majalisun dokoki da kuma yawan jihohi,” a cewar Buhari.

Exit mobile version