Site icon Muryar 'Yanci

Zaben Kananan Hukumomin Kaduna Ya Tabbatar Da Adalcin El Rufa’i – Yaro Mai Kyau

An bayyana cewar ko shakka babu zaben kananan hukumomi da aka gudanar. Jihar Kaduna kwanan nan wanda jam’iyyar adawa ta PDP ta yi nasara a maza?ar El Rufa’i, ya nuna a fili cewar El Rufa’i adali ne.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ?an majalisa mai wakiltar maza?ar Unguwar Sunusi a majalisar dokokin Jihar Kaduna Alhaji Auwal Yahaya wanda aka fi sani da suna Auwal Yaro Mai kyau a yayin tattaunawar shi da manema labarai a Kaduna.

?an Majalisar ya ?ara da cewar a baya can zamanin mulkin PDP abu ne ba mai yiyuwa ba jam’iyyar adawa ta yi nasara a za?e musanman za?en Kananan Hukumomi wanda Hukumar zabe ta jiha ce ke shiryawa ba.

Yaro Mai kyau ya cigaba da cewar Jam’iyyar El Rufa’i ta APC ita ce tayi nasara a matakin shugabancin karamar hukumar Kaduna ta Arewa da mafiyawan kananan hukumomin jihar, wanda hakan bai rasa nasaba da irin kwazo da bajintar da gwamnan ke dashi ne a bangaren jagoranci.

“Mutane irin su El Rufa’i Najeriya ke bukata wadanda suka sadaukar da rayuwar su wajen inganta ta sauran jama’a, idan aka same shi a matsayin magajin Buhari a shekarar 2023, tabbas Najeriya za ta kai ga tudun mun tsira”.

Exit mobile version