An bayyana zaben da aka yi wa Gwamna Jíhar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin Shugaban ?ungiyar gwamnonin Najeriya da kuma Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin Shugaban ?ungiyar gwamnonin Arewa a matsayin wata babbar nasara a mulkin dimukura?iyya.
Honorabul Benjamin Kalu ne ya bayyana hakan a sakon taya murna da ya aikewa gwamnonin bisa samun nasarar samun mukaman suka yi.
“Ina fatan ?ar?ashin shugabancin ka na Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya za a shawo kan muhimman batutuwa da suka shafi yankinmu ta Arewa da na Najeriya fannin tsaro da Noma da kiwo.
Hakazalika a shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya na yi imanin cewa jajircewarka a siyasa da ciyar da jihar Gombe gaba ya sa ake za?e ka, kuma muna da tabbacin za ka Kaita yankin arewa gaba.

