Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya ce abubuwa ba su rikice wa APC ba.
Shugaban Jam’iyyar ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar na zaben fitar da Gwani da ake yi a dandalin wasanni na Eagle Sqaure dake babban birnin tarayya Abuja.
Abdullahi Adamu ya bayyana cewa abubuwa suna gyaruwa a jam’iyyar kuma akwai ha?in kai haka kuma ya ce APC na magana ne da murya ?aya.
Tuni Shugabàn ?asa Muhammadu Buhari da uwargidansa Aisha Buhari da sauran manyan jiga jigai na jam’iyyar suka hallara filin domin shaida yadda za ta wakana a yayin za?en fidda gwanin.
‘Yan takara 23 ne daga sassa daban daban na kasar suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasar, sai dai wasu rahotannin dake shigo mana na bayyana wasu daga cikin ‘yan takarar sun janye a lokacin da ake tsaka da gudanar da za?en.

