Masu sa ido a za?e daga ?asashen renon Ingila sun iso Abuja, babban birnin Najeriya, gabanin babban za?en ?asar na shugaban ?asa da kuma ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar.
Kungiyar ta kunshi mutum 16 da suka fito daga ?asashen renon Ingila wanda ya kunshi ‘yan siyasa da jami’an diflomasiyya da masana bangaren shari’a da masu kare hakkin ?an adam da kuma daidaiton jinsi.
Da yake jawabi ga manema labarai a yau Litinin, shugaban kungiyar wada kuma shi ne tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki, ya ce kudurinsu shi ne sa ido da kuma duba shirin da aka yi kafin za?e da ayyukan ranar za?e da kuma bayan za?e.
Mista Mbeki ya lura da cewa za?ukan Najeriya za su kasance manya a nahiyar Afirka kuma sakamakonta na da matukar muhimmanci ga ?aukacin nahiyar.
A don haka ya bu?aci jam’iyyun siyasa a ?asar da ‘yan takara da kuma magoya bayansu da su tabbatar da ganin an yi za?ukan ranar 25 ga watan Febrairu cikin koshin lafiya da kuma gaskiya.

