Site icon Muryar 'Yanci

Zaben 2023: INEC Ta Toshe Dukkanin Hanyoyin Magudi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar za?e mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da yin garambawul na canza wasu shugabanninta na jihohi, a daidai lokacin da ake fuskantar babban zabe na kasa.

Hukumar ta canza wa wasu shugabanninta na jihohi (RECs) guda biyar daga inda suke aiki zuwa wata jihar, Festus Okoye, kwamishinan hukumar na ?asa kuma shugaban kwamitin ya?a labarai, shine ya sanar da haka ranar Lahadi a Abuja, ya kara cewa canjin ya shafi wasu daraktoci hu?u.

READ ALSO Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na’urar Za?e Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa’i Ya Magantu Ba Maganar Magudi a 2023: INEC Ta Yi Muhimmin Garbawul a Wasu Jihohi Hoto: dailytrust.com Source: UGC

A cewar Okoye, sabon jadawalin aikin ya maida REC na jihar Osun, Mr. Olusegun Agbaje, zuwa jihar Ogun, yayin da takwaransa na jihar Ogun, Farfesa AbdulGaniy Olayinka Raji, zai maye gurbinsa a Osun.

“REC na jihar Bayelsa, Dr. Cyril Omorogbe, zai koma jihar Cross Rivers yayin da na jihar, Emannuel Alex Hart zai maye gurbinsa a Jihar Bayelsa.” “Hakanan an maida shugaban INEC na jihar Zamfara, Dr. Asmau Sani Maiku?i, zuwa jihar Kaduna.”

Hukumar ta kuma bayyana cewa daraktan wayar da kan masu ka?a kuri’a, Mr. Nick Dazang, ya tafi hutun zango bisa haka Mr. Victor Ayodele zai maye gurbinsa. Hakanan kuma INEC ta sanar da maida, Mista Mikah Thabbal Lakumna zuwa matsayin daraktan sashin shugabanci, daga matsayinsa na daraktan tsaro.

Hukumar tace, Mista Nduh Lebari Samson, zai koma matsayin daraktan tsaro daga ofishin sakataren INEC, yayin da daraktan sashin ayyukan za?e, Yakubu Muhammed Duku, zai koma jihar Neja a matsayin sakatare.

Exit mobile version