Site icon Muryar 'Yanci

Za Mu Yi ?e?e Da ?e?e A Babban Za?e Dake Tafe – INEC

Shugaban Hukumar Za?e mai zaman kanta ta ?asa Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take game da zuwa za?en zagaye na biyu na shugaban ?asar idan har ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba.

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban za?en ?asar da ke tafe a Chatham House da ke birnin Landan a Birtaniya.

Ya ?ara da cewa a INEC ta yi shirin yiyuwar zuwa zagaye na biyu a za?en shugaban ?asar, kamar yadda take yi a za?uka uku da suka gabata.

Shugaban hukumar za?e ya kuma ce za?en ?asar da za gudanar cikin wannan shekara za?e ne na matasan ?asar.

Farfesa Yakubu ya kuma ce rajistar masu ka?a ?uri’a ta nuna cewa matasa ne suka mamaye adadi mafi yawa na masu rajistar za?en.

Shugaban Hukumar ya ce ya ji da?in yadda mutane suka fito domin kar?ar katinan za?ensu, yana mai cewa fiye da mutum 600,000 sun kar?i katinansu a jihar Legas ka?ai cikin watan da ya gabata.

Ya ?ara da cewa a yanzu adadin masu rajistar za?e a Najeriya sun kai miliyan 93.4, kuma daga ciki miliyan 37 wato kashi 39 na rajistar za?en matasa ne ‘yan tsakanin shekara 19 zuwa 34.

Ya kuma tunasar da maharta taron cewa hukumar za ta tsayar da rabar da katin za?en daga ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.

2- Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Rijistar Sabuwar ?ungiyar Malaman Jami’a

Gwamnatin tarayyar ta kammala yi wa sabuwar ?ungiyar malaman jami’o’i ta ?asar mai suna ‘Congress of University Academics’ (CONUA).

Ministan ?wadago na ?asar Dakta Chris Ngige, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim ?adan bayan tattaunawar sirri da shugabannin sabuwar ?ungiyar ?ar?ashin jagorancin shugabanta Niyi sunmonu.

Ministan ya kuma garga?i sabuwar ?ungiyar da cewa kada ta ?auki hanyar da takwararta ta ‘Academic Staff Union of Universities’ (ASUU). ta bi

Ya umarci ?ungiyar da ta yi aiki a duka jami’o’in ?asar ba tare da fargabar kowa ba, yana mai cewa gwamnati ta ?auki matakin kawar da ‘katutun’ da ASUU ta yi tare da lalata tsarin jami’o’in ?asar.

A shekarar da ta gabata ne dai aka ?ir?iri sabuwar ?ungiyar lokacin da kan malaman jami’o’in ?asar ya rabu kan yajin aikin da ?ungiyar ASUU ta share kusan wata takwas tana gudanarwa a fa?in ?asar.

Exit mobile version