Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzi?in zamani, Dr. Isa Pantami, ya bayyana shirinsa na samar da a?alla cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) ?aya a kowace jiha kafin ?arewar 2022,
Ministan ya fa?i haka ne a wajen ?addamar da sabon tsarin tattalin arzi?in zamani rukuni na 10 a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar Pantami, an ?addamar da ECC 23 a fa?in Najeriya, kuma akwai ragowar 13 da ake cikin aikin su. Rahoton BBC ya nuna cewa tuni ministan ya bu?e ofishin farko a wannan tsarin a jihar Katsina matakin da ya bai wa sama da mutum 40 aikin yi.
“A cikin shekaru biyu, mun bu?e sabbin Cibiyoyin amsa kiran gaggawa 23 a fa?in Najeriya, kuma kawai sauran 13 dake tafe.” “Tsarin da muka yi shine a samar da a?alla ECC ?aya a kowacce jiha dake fa?in Najeriya kafin ?arshen shekarar 2022.”
“Wa?annan cibiyoyin suna da matu?ar amfani, Lamba ce da zakai amfani ita kyauta, idan ka kira lambar ba za’a caje ka ko sisi ba.”
Pantami ya kara da cewa wannan tsarin zai taimaka wa yan Najeriya wajen bada ha?in kai da taimaka musu wajen isar da sa?on gaggawa musamman akan tsaro.

