Shugaban hukumar za?e ta ?asa Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa da ‘yan ?asar cewa za a yi amfani da na’urar BVAS a za?en gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da ke tafe a makon gobe.
Farfesa Yakubu ya tabbatar da haka ranar Asabar a lokacin ganawa da kwamishinonin hukumar za?e na jihohi a shalkwatar hukumar da ke Abuja babban birnin ?asar.
Ya ce za a yi amfani da na’urar BVAS a za?en, domin kuwa a cewarsa ana sake duba na’urorin domin kauce wa matsalolin da suka bayar a wasu wuraren a za?en makon da ya gabata.
A ranar za?e za a yi amfani da na’urar BVAS domin tantance masu ka?a ?uri’a da tattara sakamakon za?e,” in ji Yakubu
Aiki da na’urar ta BVAS ya taimaka wajen tsabtace aikin tantance masu za?e kamar yadda muka gani a za?ukan da suka gabata”.
”Tun makon da ya gabata, hukumar za?e ta ?ara ?aimi wajen sake duba na’u’rorin domin kauce wa matsalolin da aka samu a wasu wuraren a za?en da ya gabata, musamman kan ?ora sakamakon za?e a rumbun adana sakamakon da muka tanadar a shafin intanet. Kuma muna da tabbacin cewa na’urorin za su yi aiki kamar yadda ya kamata.”

