Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalar tsaro a kasar, hukumomi sun sha alwashin kawo karshen matsalar daga nan zuwa watan Disamba mai zuwa.
Wannan na ?unshe cikin jawabin da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya yi lokacin wani taron hadin gwuiwa da wasu takwarorinsa ministoci domin yin karin haske kan matakan da gwamnatin kasar ke dauka don kare al’umma
Rauf Aregbesola ya ce ”Babbar manufarmu ita ce mu murkushe su baki daya, sannan mu dawo da cikakken zaman lafiya mai dorewa a dukkan fadin kasarmu Najeriya.
Kuma ina tabbatar muku, abin da za mu yi ke nan in sha Allahu, nan da watan Disambar wannan shekarar”
Da gaske muke, kuma ku rubuta ku ajiye, mun jajirce domin kawar da matsalolin tsaro daga dukkan sassan Najeriya. Akwai wannan niyyar, kuma an bayar da umarni domin cimma haka.

