Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, yace za’a saka fasahar 5G a Najeriya a watan Janairu na shekara mai kamawa ta 2022.
Ministan ya bayyana cewa fasahar ta 5G zata taimaka matu?a gaya wajen rage aikata manyan laifuka na lalata kayayyakin gwamnati da sauran ayyukan ashsha.
Pantami ya fa?i haka ne a Maiduguri, ranar Alhamis, a wurin taron da ma’aikatar ya?a labarai ta shirya kan lalata kayan ?angaren sadarwa da wutar lantarki.
Ministan, wanda daraktan fasaha na hukumar sadarwa (NCC), Ubale Maska, ya wakilta, yace ba da jimawa ba majalisar zartarwa ta ?asa ta amice da sanya fasahar 5G a Najeriya.
Bugu da ?ari, ministan yace fasahar zata taimaka wajen ?ara kulawa da yan ta’adda dake lalata manyan kayayyakin gwamnati a fa?in ?asa, domin za’a ?auki matakin kame su da fasahar. Ya kuma bayyana cewa akwai sashin yanar gizo na sadarwa 50,000 a fa?in Najeriya, kuma saka fasahar zai taimaka sosai wajen amfani da su.

