Site icon Muryar 'Yanci

Za Mu Karkashe Ragowar ‘Yan Boko Haram Muddin Basu Mika Wuya Ba – Shugaban Dakarun Soji

Rahotanni daga Hedikwatar tsaro dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar sojin Najeriya ta bu?aci ragowar mayakan Boko Haram da su mi?a wuya su rungumi zaman lafiya, ko su fuskanci mummunan kisa na ?are dangi.

Babban Kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Nijeriya, Birgediya Janar A.A. Eyitayo ne ya yi wannan kiran a wajen wani biki da sojoji suka shirya wa ?an jarida a ranar Lahadi a Maiduguri.

Eyitayo, wanda kuma shi ne Kwamandan ?aya daga cikin rundunar Operation Hadin Kai, ya ce sun fatattaki maya?an a farmakin da sojoji suka kai wanda ya jefa ragowar maya?an da suka tsira cikin ru?ani.

Ya yi kira ga sauran maya?an su rungumi zaman lafiya su mi?a wuya domin a cewarsa “mu kan mu ba su zubar da jini, babu wanda yake so ya ga mutane na mutuwa.”

Exit mobile version