Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Enugu na bayyana cewar wasu yan bindiga da ke taaddanci a kudu maso gabashin kasar sun fitar da wani faifan bidiyo, inda suke gargadin Gwamnatin Buhari da kada ta sake ta gudanar da zaben shekarar 2023 a yankin.
Wannan ne karon farko da kungiyar taaddanci ta saki faifan bidiyo tun da ta fara kaddamar da hare hare a kudu maso gabashin Najeriya da wasu yankunan kudu maso kudu.
A cikin bidiyon, wanda ya karade shafukan intanet, yan bindigar sun yi korafi ne a game da ci gaba da tsare jagoran kungiyar da ke neman kafuwar kasar Biafra, Nnamdi Kanu da hukumomin kasar ke yi.
A cikin bidiyon da aka fitar a ranar 21 ga watan Afrilu, an ga wasu mutaane 4 da suka rufe fuskokinsu a cikin wani kungurmin daji, a yayin da daya daga cikinsu yake Magana cikin fushi.

