Site icon Muryar 'Yanci

Za A Yi Wa Magu Karin Girma Zuwa Mataimakin Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kula da al’amuran ‘yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda a cikin wannan makon.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan ‘yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Mai Shari’a Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

An zargesa da bata da duk wata shaida tare da hanawa tare da dakile duk wasu hanyoyin bincike a wani bincike da ake yi da ya hada da tsohon shugaban majalisar tarayya da tsohon manajan darakta PPMC.

Amma kuma, bayan da kwamitin ya mika rahoton a watan Nuwamban 2020, kadan daga cikin shawarwarinsu aka aiwatar. Magu, wanda har yanzu bai saki jiki ba bayan binciken kwamitin, an gano cewa yana da alaka mai kyau da shugaban hukumar kula da lamurran ‘yan sanda, Musiliu Smith, tsohon sifeta janar na ‘yan sanda daga jihar Legas.

Exit mobile version