Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin Islaman nan da ke daawar yi wa ?an fashin daji masu satar mutane waazi, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa za a yi da na-sanin ayyanasu a matsayin’ yan ta’adda.
Malamin ya fa?i haka ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a wani shafinsa na Facebook.
Tuni dai ?an majalisa a Najeriya suka nemi gwamnatin Tarayya ta ayyana ?an fashin da suka addabi arewacin Najeriya a matsayin ?an taadda.
A cikin sanarwar, Sheikh Gumi ya yi garga?in cewa da zarar an ayyana ?an fashin daji a matsayin ?an taadda ?ungiyoyi masu daawar jihadi na ?asashen waje za su samu gindin zama.
Ya kuma ce wannan zai iya janyo raayin matasan da ke fama da rashin aikin yi.
“Babu wanda ke shakkar cewa son raine a yau ya mamaye siyasarmu. Don ci gaba, dole ne wasu su fito su yi magana, a cewar Sheikh Gumi.
Sai dai kuma a cikin bayanansa malamain ya ce ayyukan da ?an fashin daji ke aikatawa sannu a hankali sun na taaddanci saboda duk inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, taaddanci ne tsantsarsa.

