Site icon Muryar 'Yanci

Za A Yi Ambaliyar Matalauta A Najeriya Nan Da Shekaru Uku – Bankin Duniya

Babban bankin Duniya ya yi wani hasashe akan ?asar Najeriya na fuskantar ba?in talauci da koma baya a tattalin arziki gami da hauhawar adadin matalauta a kasar nan da shekaru uku masu zuwa muddin ba a dauki matakan da su ka dace ba, na hana afkuwar hakan.

An ruwaito bankin Duniya ya na cewa muddin ba a cigaba da tafiya a kan dabarun ceto kasar ba, Najeriya za ta dade a matsala mafi muni irin wadda ba’a ta?a gani ba tsawon shekaru 40 a tarihin ?asar.

“Nan da shekaru uku, akasarin ‘Yan Najeriya na iya ganin ci-bayan nasarorin cigaban tattalin da aka samu na shekaru, kuma kasar na iya fada wa cikin matsin da ya fi kowane tun 1980.”

A cewar Babban Bankin na Duniya kasar na iya guje wa wannan matsala idan aka dage wajen bin manufofi da tafarkin da su ka dace. An fitar da wannan bayani ne da taken: “Rising to the Challenge: Nigeria’s COVID-19 response”.

Babban Daraktan Babban Bankin Duniya a Najeriya, Shubham Chaudhuri ya ce kasar tana cikin ga?a mai wuya na daukar matakin da zai kai ta ga ci ko akasin haka. “Babu tabbacin dawowa daidai a 2021, kuma hakan ya danganta da matakan da aka dauka.

Shubham Chaudhuri ya ce Talakawa a Najeriya za su karu da yawan da ya kai Miliyan 20 a 2022.

Hasashen yace za ayi fama da karancin abinci a lokacin da ake fuskantar annobar COVID-19 da karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin Duniya.

Exit mobile version