Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ri?a kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar yan makarantar firamare miliyan 10 a kowace rana a shirin ta na ciyar da ?alibai, wato National Home Grown School Feeding Programme (NHGSFP) da ta ke gudanarwa a duk fa?in ?asar nan.
Shugabar gungun maaikatan da ke gudanar da shirin, Hajiya Aishatu Digil, ita ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi kan hanyoyin rarraba abincin da sake duban fasalin ku?in da ake kashewa a shirin.
Ta ce Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta samo amincewar a ri?a kashe N100 a kan kowane yaro a kullum a shirin.
Ta ?ara da cewa daga yanzu, za a ri?a kashe N100 a kullum wajen ciyar da kowane daga yan makaranta 9,990,862 yan ajin firamare ?aya zuwa aji uku da ke cikin shirin da a kullum a tsawon kwana 20 a wata, wanda jimillar ku?in ya kama N999,086,200 a kullum.
Ta ce, A da kafin yanzu, mu na kashe N70 ne wajen ciyar da kowane yaro, a abinci zaman ci ?aya. Haka mu ke yi tun daga 2016, amma yanzu shugaban ?asa ya amince a ?ara ku?in zuwa N100.
Mu na da masu ruwa da tsaki irin su Shirin Abinci na Majalisar ?inkin Duniya (World Food Programme), da Hukumar ?ididdiga ta ?asa (National Bureau of Statistics), da Hukumar Fa?akarwa ta ?asa (National Orientation Agency, NOA), da ?ungiyar Inganta Abinci ta Duniya (Global Alliance for Improved Nutrition, GAIN), da Maaikatar Aikin Gona da ta Ilimi, da ma wasu, da za su tattauna kan hanyoyin rarrabawar.
Mun taru a nan ne domin mu kalli hanyar da ta fi dacewa mu yi amfani da ita wajen samun alfanun shirin bisa sabon tsarin kashe ku?i don inganta kyawun abinci da ake ba yaran.
Lissafin kashe N100 ?in shi ne: N70 shi ne ku?in dukkan kayan ha?a abincin amma ban da ?wai, sai N14 ku?in ?wai da za a ri?a saye ta hanyar gwamnatocin jihohi da ha?in gwiwar ?ungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya (Poultry Association of Nigeria).
Mu na tsara fitar da ranar da za mu kira Larabar Cin ?wai (Egg Wednesday), inda za a ri?a ba kowane yaro da ke cikin shirin ?wai guda ?aya a kowace ranar Laraba; sai N10 ta ladar masu girki, N5 da N6 na tabbatar da lafiyar abinci wanda za a ri?a ba masu girkin, da kuma naira ?aya ta tabbatar da inganci, wadda za a ba jamiai masu sa ido, wanda wannan za?i ne.
Digil ta ce shirin zai tabbatar da an tsame muggan halayen aiwatarwa, ta ?ara da cewa maaikatar na so ta kawo gyare-gyare.
Ta ce, Bayan wannan taron, za mu tattaro shawarwarin masu ruwa da tsaki, sannan mu mi?a su ga minista saboda mu aiwatar da sabon tsarin ku?in ciyarwar, wanda zai fara daga wannan watan.

