Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar wakilai ta bu?aci gwamnatin tarayya ta samar da kyamarorin da za a ri?a ?aurawa a jikin jami’an tsaro, kuma a kafa cibiyoyin sa ido a kan aikace-aikacensu a fa?in ?asar.
A cewar majalisar sanya wa jami’an tsaro kyamarori, zai taimaka wajen rage ?orafe-?orafen keta ha??in ?an adam da kuma tozarta ikon da doka ta ba su.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja ?an majalisar wakilai Hon. Abubakar Yunus, yace dalilin daukar wannan matakin, shi ne yadda korafe-korafe suka yi yawa kan jami’an ‘yan sandan kasar ta fuskar amfani da karfi fiye da kima ga farar hula.
”Ana son tabbatar da aiki ingantacce, kuma bisa tsari ba tare da wata kumbiya-kumbiya da cuku-cuku irin na jami’an tsaro, wannan shi ne abin da wannan doka ta ke son kawarwa.
Babban dalilin da ya sanya muke so yin hakan a wanna zamani shi ne tuhume-tuhume sun yi yawa kan ‘yan sandan Najeriya, wanda ake ganin su na kisa ba gaira ba dalili, kuma yawanci idan abu ya faru sai ka ji sun ce wai an yi domin tsare kan su,” in ji Honarabul Yunus.
Ya kara da cewa a wasu lokutan za a ga jami’an kwastam sun harbe mutum, ko jami’an ‘yan sanda a wurin binciken ababen hawa su harbe mutum, da dai sauran lamura da ke faruwa irin hakan.
Wadannan na daga cikin dalilan da majalisa ta kawo dokar ta yadda idan suka aikata wanna kamarar da ke jikinsu za ta nadi duk wani motsinsu ta yadda za a san halin da suke ciki a wuraren aiki.

