Site icon Muryar 'Yanci

Za?en Edo: Za Mu Yi Amfani Da Rajistar 2019 Ne – INEC

Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) za ta yi amfani ne da rajistar masu za?e ta 2019 wajen gudanar da za?en gwamna da za a yi a Jihar Edo.

Ya ce za a yi hakan ne saboda annobar korona, wato COVID-19.

Kwamishinan hukumar za?en wanda ke da zama a jihar, Dakta Johnson Alalibo, shi ne ya bayyana haka a wani zaman tattaunawa da aka tsakanin hukumar da ?ungiyoyi masu zaman kan su su sama da 70 a Abuja.

A cewar Alalibo, akwai jimillar masu za?e da aka yi wa rajista su 2,210,534 a Edo, yayin da an kar?i katin za?e guda 1,726,738.

Ya ce: “Hukumar ta ?age kar?ar katin masu za?e tare da yi wa masu za?e rajista saboda annobar cutar korona. Saboda haka, za mu koma ga abin da mu ka yi amfani da shi a babban za?en 2019, shi za mu yi amfani da shi.

“Tun daga lokacin da aka bayyana jadawalin ranakun za?en Edo, ayyuka daban-daban da su ka danganci za?en sun lullu?e hukumar, kama daga sa ido kan za?u??ukan share fage na jam’iyyun siyasa zuwa buga fom-fom masu ?auke da sunayen ‘yan takara.

“Mun kar?i wasu daga cikin kayan aiki kuma har yanzu mu na kar?ar su tare da rarraba su a Yankunan ?ananan Hukumomi.

“Mun samu ?arancin na’urorin karanta katittikan za?e masu ?wa?walwa, mun bu?ata kuma an kawo mana daga wasu jihohin. Mun gama auna na’urorin tare da buga rajistar masu za?e.’’

Alalibo ya ?ara da cewa shi ma aikin horas da ma’aikatan za?e da jami’an tsaro, wanda aka raba a matakai uku, an kammala shi.

Ya ce an gama tsara yadda za a taimaka wa na?asassu su yi za?en, kuma an yi masu isasshen tanadi.

Ya ce akwai shirye-shiryen fa?akarwa da ake yi yanzu a rediyo da sauran yekuwa don ?arfafa wa mata gwiwa su fito su yi za?e su ma.

Ya ?ara da cewa an tanadi na’urorin auna zafin jiki, da maganin wanke hannu da bokitai saboda za?en.

Alalibo ya ce hukumar ta gano wuraren da ke da yiwuwar aukuwar tada hankali a lokacin za?en kuma ta sanar da hukumomin tsaro don a kauce wa tashin hankali.

Ya ?ara da cewa hukumar za?en za ta gudanar da za?e wanda kowa zai yi na’am da shi.

Tun da farko, sai da jagoran ?ungiyoyin masu zaman kan su, wa?anda su ke kiran kan su ‘Nigerian Civil Society Situation Room’, Mista Clement Nwankwo, ya yi bayanin cewa manufar zaman tattaunawar ita ce saboda manyan masu ruwa da tsaki a za?en da kwamishin za?en (wato Resident Electoral Commissioner, REC) su fahimci inda aka sa gaba da inda ya kamata su maida hankalin su don tabbatar da an yi za?e kar?a??e a Edo.

Ya ce, “Mun san cewa akwai damuwa sosai game da za?u??ukan a yanzu haka, damuwa game da barazanar tashin hankali na da?a tasowa; mu na fatan wannan za?e duk da fargabar da ke akwai za a yi shi cikin lumana.

“Daga ?angaren mu na ‘yan ‘Situation Room’, mun yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, wa?anda su ka ha?a da ‘yan takara, jam’iyyun siyasa, da ma duk wani wanda ke da hannu a za?en, cewa akwai muhimmiyar bu?atar a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Saboda haka mu na kira da babbar murya da a kula da zaman lafiya kuma a kula da masu za?e saboda idan har babu zaman lafiya to mu na da babban ?alubale.”

Nwankwo ya ce ?ungiyoyin sun tattauna da Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, kuma ya ba su tabbacin cewa hukuma ce mai zaman kan ta wadda ba ta da wani ?an lele a za?en.

Ya ce kwanan nan hukumar ta fito da wani sabon tsari inda masu za?e za su ga sakamakon ?uri’un da su ka jefa da zaran an tattara su a waje guda.

Ya ce wannan sabon tsari wani cigaba ne a aikin za?e, wanda ?ungiyoyin sun yi murna da shi.

Ya ?ara da cewa, “Fatan mu shi ne ba za a wargaza wannan sabon tsarin ba.’’

Nwankwo ya ce ?ungiyoyin sun sa ido su ga an yi za?e wanda zai tabbatar da cewa an magance matsalolin da ?ungiyoyin na ‘Situation Room’ su ka damu da su game da za?en.

Ya ce ?ungiyoyin za su tura ‘yan sa ido mutum 300 a rumfunan za?en da wuraren ?irga ?uri’a don su ga yadda aikin za?en ke gudana.

Ya yi kira ga INEC da ta aiwatar da za?e wanda kowa zai yi murna da shi, tare da ?aukar darussa daga babban za?en da aka yi a ?asar nan a cikin 2019 kuma su inganta shi daga yanzu zuwa manyan za?u??ukan da za a yi a cikin shekara ta 2023.

Exit mobile version