Sakataren APC na rikon-kwarya, Sanata John Udoedeghe ya yi kira ga ya yan jamiyyarsa da su yi kokari wajen ganin sun samu nasara a zabe mai zuwa. John Udoedeghe ya ce zuwa babban zaben 2023, lokacin da mutane za su shige inuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wuce.
Sakataren jamiyyar mai mulki ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya zauna da wata kungiya ta magoya bayan APC a karkashin Frank Ossai.
An yi wannan zama ne a babban sakatariyar jamiyyar APC da ke birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2020.
Udoedeghe ya ke cewa: Dukkanku da ke siyasar kasa; ku tabbatar an cigaba da damawa da ku a mazabunku, da kananan hukumomi, da kuma jihohinku.
A 2023 ne shugaba Buhari zai kammala waadinsa na shekaru takwas. Ana tunanin cewa APC ta na samun damar lashe zababbuka a matakai da-dama saboda sunansa.
Sanatan na jihar Edo ya gargadi magoya bayan jamiyyar da cewa: A zaben 2023, shugaba Muhammadu Buhari ba zai fito a cikin masu takara ba. Dan siyasar ya kuma shaidawa fusatattun yan jamiyyar APC cewa kwamitinsu na rikon kwarya a shirya ya ke da ya yi wa kowa adalci wajen dinke barakar da jamiyyar ke fama da ita.
Kafin nan, shugaban tafiyar, Frank Ossai ya yi kira ga kwamitin rikon da ya duba aikin da Sanata Ken Nnamani ya taba yi domin kawo zaman lafiya a APC.

