Wani rahoto da ke zuwa mana ya yi ikirarin cewa babbar jamiyyar mai mulki ta APC na zawarcin tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, domin ya fito takarar Shugaban kasa a inuwarta a 2023.
Rahoton wanda jaridar This Day ta kawo ya yi ikirarin cewa wasu shugabannin jamiyyar na matsawa tsohon Shugaban kasar a kan ya duba yiwuwar amsa tayin.
Jaridar ta bayyana cewa wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta ta ce gwamnonin APC wadanda suka ziyarci Jonathan don taya shi murnar cika shekaru 63, sun yi amfani da taron wajen yi masa tayin kujerar shugabancin kasar.
Rahoton ya ci gaba da ikirarin cewa makusantan Buhari na goyon bayan yunkurin ganin Jonathan ya zama Shugaban kasa a 2023.
A cewar rahoton, makusantan Buhari sun yarda cewa Jonathan ba zai cutar da raayin kungiyarsu ba saboda haka shine ya cancanci karban mulki idan aka mika ta kudu.
Wata majiya a ?angaren Buhari wacce bata so a bayyana sunanta ba tace: Ya mika mulki cikin lumana sannan bai riki kowa ba saboda haka ba zai zama barazana ga raayin arewa ba.
Sai dai, a baya Jonathan ya sha karyata cewar yana da raayin takarar Shugaban kasa. Tsohon Shugaban kasar ya bayyana ?arara cewa ya mayar da hankalinsa ne a kan gidauniyarsa.

