Site icon Muryar 'Yanci

Yunwa Na Hallaka ‘Yan Gudun Hijira A Katsina

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar kimanin mutane Ashirin da uku ne suka rasa rayukansu a sanadiyar yunwa, hawan jini, damuwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake ?aramar hukumar Jibiya a jihar.

Shugaban Sansanin ‘yan gudun hijirar Sa’adu Salisu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karamar hukumar ta Jibiya ranar Talata.

A wani rahoto da kungiyar cigaban karamar hukumar Jibiya ta fitar na ranar Litinin, ya nuna cewa, akalla ‘yan gudun hijira dubu ashirin da biyu, da dari uku da sittin da biyar (22,365) daga yankunan Shimfida, Garin Maiwuya, Garin Zango, Garin Kwari da kauyukan Tsambaye suna zaune ne cikin garin Jibiya.

‘Yan gudun hijirar na samun mafaka ne a makarantar sakandiren ‘yan Mata ta gwamnati da ke Jibiya.

Kazalika Shugaban sansanin ‘yan gudun hijirar, Sa’ad Salisu ya bayyana cewa akalla mata 35 ne suka haihu a sansanin a cikin watanni hudu da suka gabata, yana mai cewa adadin zai iya zarce haka, nan gaba kadan.

A gefe guda kuma, wani lamari mai tayar da hankali kamar yadda Salisu ya bayyana, shi ne yadda akasarin yaran da ke garin da kuma na sansanin ba sa iya samun ilimi.

Ya ?ara da cewa, akwai yara sama da dubu uku (3,000) a sansanin da suka bar yankunan su da suke amma yanzu ba sa iya zuwa makarantar, saboda gwamnati ba ta tanadar musu da makaranta ba a sansanin da suke zaune.

Sai dai Salisu ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta daukar matakin maido da tsaro a cikin yankunan da harin yan bindiga ya ?ai-?aita, domin su koma gudanar da rayuwa kamar yadda suka saba.

Exit mobile version