Shugaban ya bayyana haka ne a jawabi a wani biki kan magance ?arancin abinci ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar Neja.
Da yawa daga cikin mukarraban gwamnatin Tinubu ciki har da ministan ku?i Wale Edun, sun ?ora laifin matsalolin tattalin arziki da kuma tsaro da ?asar ke fuskanta a kan gwamnatin tsohon shugaban ?asa Muhammadu Buhari.
Sai dai Tinubu, wanda ya kar?i ragamar mulki daga hannun Buhari a watan Mayun bara, ya ce damuwarsa ba wai ya zargi gwamnatocin da suka gabata ba, illa ?ullo da tsare-tsaren da suka dace domin ?ora ?asar kan turbar ci gaba.
Najeriya dai na fama da matsalar garkuwa da mutane don neman ku?in fansa, hauhawar farashin kayayyaki, tashin farashin dala, matsalar tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur, lamarin da ya janyo zanga-zanga a sassan ?asar.

