Iyalan malamin addinin Musuluncin nan da aka yi wa kisan gilla a jihar Yobe Sheikh Goni Aisami, sun bayyana damuwarsu ga yadda suka ce har yanzu ba a gurfanar da wadanda ake zargi da kashe shi a gaban kotu ba kusan kwana hamsin da faruwar lamarin.
Wani soja ne da malamin ya rage wa hanya ake zargi da harbe shi domin ya sace motarsa yayin da malamin ke kan hanya daga Kano zuwa Gashua.
Sai dai hukumomi sun ce nan ba da jimawa ba za a soma shariar gadan-gadan.
?aya daga cikin iyalan marigayin ya ce ba su ga dalilin da zai sa a yi tsaiko wajen hukunta wa?anda ake zargi ba.
Abdullahi Goni Aisami ya ce sun shiga tashin hankali saboda rashin jin wata hujja daga hukumomi kan abin da ya sa aka ?i hukunta mutanen.
“?Muna cikin ba?in ciki da takaici, su daga ?angaren matan malam, hankalinsu ya fi na kowa tashi saboda suna ganin kamar an ma ?i yin hukuncin ne haka kawai, in ji shi.
D?aga ?angaren hukuma kuwa, kakakin rundunar ‘?an sanda na jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya ce bayan sun gama bincike suka tura wa hukumar shari’a ta jihar domin tabbatar da cewa an gurfanar da wa?annan sojoji guda biyu gaban kotu.
“An yi nasarar haka, inda ranar 19 ga watan Satumba aka gabatar da su a gaban kotu, kuma kwamishina da kansa ya zama lauya mai gabatar da ?ara na gwamnati,” a cewarsa.
“?Ya gabatar da hujjojinsa da shaidunsa gaba ?aya a gaban kotu inda wa?anda ake zargi suka ce su ba su da laifi, sannan aka tsaya daga nan aka rufe ?arar, za a sake sauraron shari’ar a zama na biyu.
D?SP Dungus ya ?ara da cewa lokacin da aka yi zaman shari’ar kotunan Najeriya suna hutu, kuma “muna tunanin idan sun dawo hutu, za su gaya mana ranar da za a sake dawo da sojojin zuwa kotun.

