Gwamnan Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya yi wa fursunoni 115 afuwa, wa?anda aka za?o daga gidajen yari daban-daban da ke fa?in jihar.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa afuwar ta biyo bayan wani nazari da kwamitin da aka kafa kan hakkin jin kai karkashin jagorancin tsohon babban lauyan gwamnati kuma babban mai taimakawa gwamna na musamman kan harkokin sharia, Barista Sale Samanja ya yi.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Samanja ya ce afuwar da gwamnan ya yi ya, ta yi daidai da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin 1999 ya ba shi wanda aka yi wa kwaskwarima.
Barista Samanja ya ce mutanen da aka yi wa afuwar sun yi farin ciki da kuma gode wa gwamnan, inda suka yi alkawarin amfani da yancin da suka samu wajen gyara kura-kuran da suka yi a baya.
Da yake kar?ar rahoton kwamitin a gidan gwamnati da ke Damaturu, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana rahoton afuwar da aka yi wa fursunonin a matsayin muhimmin abu da kuma kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen rage cinkoso a gidajen gyaran hali.

