Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an tsaurara tsaro a jahoji 28 cikin jahohi 36 inda za a gudanar da za?en gwamnoni da na yan majalisun dokokin jahohi a yau Asabar.
Babban sifeton yan sandan Najeriyar, Usman Baba, ya ayyana dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jihohi daga karshe 12 na tsakar daren Jumaa har zuwa karfe shida na yammacin ranar Asabar bayan kammala za?ukan.
Rahotanni sun ce an samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan jamiyyu a Jihar Legas, inda gwamnan Jihar mai ci na jamiyyar APC, Babajide Sanwo-Olu, yake fuskantar zazzafar adawa daga ?an takarar gwamnan Jihar na jamiyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour.
Jamiyyar ta Labour ce dai ta samu kuriu mafi yawa a za?en shugaban ?asa da ya gudana watan jiya a Jihar Legas.
Shugaban Hukumar za?e Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da cewa Hukumar ta tanadi dukkanin abubuwan da ake bu?ata domin tabbatar da samun nasara a yayin zaben.

