An bayyana cewar ko shakka babu wasu ?atagarin ‘yan siyasa da wasu baragurbin malaman addini na Kirista da Musulmi sune tushen dukkanin rikice-rikicen da ya ?i ci ya ?i cinyewa a yankin Arewacin Najeriya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani fitaccen Malamin addinin Kirista mazaunin garin Kaduna mai suna Pastor Yohanna Buru a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu dangane da halin ta?ar?arewar tsaro dake addabar arewacin Najeriya.
Pastor Buru ya kara da cewa sakamakon sa?a da mugun zare da wadannan malaman addini ke yi ga mabiyansu ta hanyar rura wutar gaba da kuma son zuciya na miyagun ‘yan Siyasa dake amfani da banbance banbance jama’a domin cimma muguwar manufarsu ta siyasa shine dalilin jefa kasar Arewa a halin da take ciki.
Dangane da kiran da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi na cewar Jama’a su nemi makami domin kare kansu daga ‘yan Bindiga, Malamin addinin Kiristan yace ko kadan bai goyi bayan maganar Gwamnan ba, domin nauyi ne dake kan hukuma kula da dukiya da rayukan jama’a, daga lokacin da aka ce talaka ya ?auki makami domin kare kai to lallai an shiga wani hali.
Pastor Buru ya kuma soki lamirin mai ba shugaban ?asa shawara kan ya?a labarai Garba Shehu dake fa?in cewa wasu ne ke kokarin bata harkar tsaro domin shafawa Gwamnatin Buhari ba?in fenti, inda yace ba gaskiya bane wannan magana, gwamnati ta samu matsala na kasa sauke nauyin dake kanta ta fuskar samar da tsaro bayan alwashin da ta sha.
Hakazalika malamin addinin Kiristan ya nuna rashin gamsuwa da furucin Dattawan Arewa akan harin da ‘yan Bindiga suka kai Kwalejin NDA Kaduna, na cewar a kori mai ba shugaban ?asa shawara ta fuskar tsaro Janar Monguno.
“Korar Monguno ba zai canza komai ba, mafita shine Gwamnati ta koma ga Allah a nemi malaman addini su yi wa ?asa addu’a Allah ya kawo mana karshen dukkanin matsalolin dake addabar Najeriya”.

