Site icon Muryar 'Yanci

‘Yan Sanda Sun Cafke Matasan Aljannu Biyu A Katsina

Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar damke wadansu shahararrun ‘yan damfarar da ke make murya a matsayin fararen aljannu, inda suke kiran mutane da cewa su aljannu ne, inda suke tambayar sirrin katin fitar da kudi wato (ATM). Akwai Kabiru Bashir, dan shekara ashirin da bakwai da kuma Sadiq Ashiru, dan shekara talatin da haihuwa, dukkan su yan asalin karamar hukumar Danbatta a jihar Kano.

Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya baje kolin su gaban manema labarai a yau Laraba, a helkwatar rundunar da ke kan hanyar zuwa Daura, cikin garin Katsina.

Gambo Isa ya kara da cewa ranar 08/1/2021 ne, aka kama su, bayan sun saci katin fitar da kudi na Rabi’atu Garba, da ke karamar hukumar Mani ta jihar Katsina, inda suka kirata suka ce su aljannu ne, suna bukatar sirrin katin fitar da kudinta, idan har ta bayar za su ba ta naira miliyan daya, kai tsaye zuwa asusunta ajiyar ta da ke bankin. Da ta ji haka, sai ta hanzarta kai korafi a ofishin yan sanda da ke cikin garin Katsina, muka fara bincike sai muka kai ga nasarar cafke su. A lokacin da muke bincikar su, sun amsa laifin su, kuma sun ce ba sau daya bane suke aikata wannan damfarar ba.

An samu farar mota kirar Honda da kuma katin cirar kudi na ATM guda biyu a hannun su da katin shaidar aiki, na jami’in tsaron farin kaya (NSCDC) mai dauke da sunan Kabir Bishir da wayar hannu guda hudu da kuma tsabar kudi har naira dubu dari da ashirin da shidda a hannun su. Ana ci gaba da bincike.

Exit mobile version