Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun ku?i na naira 200 daga yanzu har zuwa 10 ga Afrilu.
A cikin jawabi da shugaba Buhari yayi ranar Alhamis, Shugaban kasa ya ce ya umarci babban bankin kasa ya wadata bankuna da sabbin takardun ku?aden don ya ishi jamaa.
Bayan haka ya umarci yan Najeriya su yi hakuri da gwamnati su bi doka cewa ba a bullo da wannan tsari ba don a muzguna wa mutane.
Daga yanzu za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun ku?i na naira 200 tare da sabbin takardun ku?in. Sai dai kuma za a dai ma amfani da su ne daga ranar 10 ga Afrilun 2023.
Buhari ya ce wannan ?afa da gwamnati ta ?aga bai hada da takardun ku?i na naira 500 da naira 1000 ba.

