Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce faduwar Najeriya a kan tsarin cin hanci da rashawa na Transparency International ya nuna ‘yan Najeriya, ba Shugaba Muhammadu Buhari ba, The Cable ta ruwaito.
A lissafin shekarar 2020 da aka fitar a ranar Alhamis, Najeriya ta sauka zuwa 149 daga cikin kasashe 180 da aka gudanar da binciken bayan sun sami maki 25 cikin 100.
Fadar shugaban kasa ta ki amincewa da matsayin, tana mai cewa bangaren TI a Najeriya ya kunshi mambobin kungiyar adawa. Lai Mohammed, ministan yada labarai da aladu, ya kuma ce rahoton ba gaskiya bane na idan akayi la’akari da kokarin da kasar ke yi na yaki da rashawa.
Garba Shehu ya bayyana hakan ne yau Litinin lokacin da yake amsa tanbayoyi a wani shiri a gidan talabijin na Channels Television na Sunrise Daily, Shehu ya ce jerin bayanan yana nuna cin hanci da rashawa ne daga yan Najeriya ba gwamnatin Buhari ba. Zan fada muku cewa wannan zancen ba hukunci bane a kan Buhari ko gwamnatinsa ko yakin da take yi da rashawa, zan fada muku cewa wannan hukunci ne a kan yan Najeriya, “Saboda idan kuka lura da abubuwan da suke amfani da su wajen fidda wannan matsaya, sun yi amfani da abubuwa guda takwas, shida daga ciki sun nuna Najeriya a matsayin sama ko kasa, Najeriya a matsayi daya, in ji Shehu.
Biyun da suka zauna a kansu, wadanda suka haifar da wannan koma baya, su ne ainihin matsalolin Najeriya. Suna magana ne game da aladun siyasa na kasar nan, siyan kuriu, yan daba. Shin Buhari ne dan daba? Ba mu yin sata. Kuma lokacin da suke magana a kan bangaren sharia, suna magana ne kan yadda ake ganin cin hanci da rashawa a bangaren sharia.
Wadannan hasashe ba da gaskiya bane. “Haka ne, akwai batutuwa a wannan bangaren amma canje-canje da yawa suna faruwa a wannan bangaren ba zai yi kyau ba idan suka yarda da shi don haka ka karfafa wa wadannan jamian shariar da suke a tsaye sannan kuma tsarin ya samu sauki.

