Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Matthew Hassan Kukah, bishop din cocin Katolikan shiyyar jihar ya ce yan Najeriya su na tuna addini ne kadai lokacin zabe.
A cewarsa duk wadanda su ke daukar matsalar tsaro a matsayin matsalar addini su na yaudarar yan Najeriya. Bishop Kukah ya ce lokacin za?e ne ka?ai ?an Najeriya suke tuna addini amma banda lokacin sata.
A cewarsa rashin tsaro zai zo karshe ne idan yan kasa sun daina ci gaba da yaudarar junansu.
Kukah ya bayyana hakan a ranar Jumaa yayin tattaunawa da manema labarai a Sokoto.

