Site icon Muryar 'Yanci

‘Yan Najeriya Miliyan 133 Na Fama Da Matsanancin Talauci – Gwamnatin Tarayya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na ?an ?asar, wato mutum miliyan 133 na cikin talauci.

Al?aluman binciken ma’aunin talauci a Najeriya ne suka tabbatar da hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Hukumar ?ididdiga ta ?asa da hukumar tsara bayar da tallafi ga masu ?aramin ?arfi da shirin samar da ci gaba na majalisar ?inkin duniya da asusun ilimin ?anana yara na Unicef da shirin ya?i da talauci da cigaban al’umma na Oxford ne suka gudanar da aikin ?ididdigar.

Binciken ya nuna cewa an kar?i bayanan magidanta dubu 56 a sassan jihohin ?asar 36 da birnin tarayya Abuja, da aka gudanar tsakanin watan Nuwamban 2021 zuwa Fabarairun 2022.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matalauta a ?asar na rayuwa ne a arewacin Najeriya, yayin da kashi 35 cikin 100, kusan mutum miliyan 47 ke nan na zama ne a kudanci.

Sokoto ce jihar da ta fi fama da talauci a ?asar, inda kashi 91 cikin 100 na al’ummarta ke rayuwa hannu-baka hannu-?warya, Ondo ce kuma mafi ?arancin talauci a Najeriya da kashi 27 cikin 100.

A lokacin da ya yi tsokaci kan al?aluman, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wannan bayani zai bijiro da hanyoyin da za a bi wajen ya?i da talauci.

A wani labarin na daba hukumar Abinci ta Majalisar ?inkin Duniya ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya miliyan 19.4 ne za su yi fama da yunwa da barazanar rashin abinci a watannin Yuni zuwa Agustan bana.

Hukumar ta yi wannan bincike tare da ha?in gwiwar Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da wasu Cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkar noma.

Rahoton ya yi nazarin matsalar ?arancin abincin da za a fuskanta da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankunan Sahel da Afrika ta Yamma.

Exit mobile version