Site icon Muryar 'Yanci

‘Yan Kwangila Na Aiki Yadda Ya Kamata A Abuja – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace hanyoyi da dama da ta bada kwantiraginsu ana cigaba da aiyikansu yadda ya kamata ba tare da wata matsalaba a fadin kasan nan baki daya.

Ministan birnin tarayya Abuja Musa Bello ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Musa Bello yace aniyar gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaba Muhammadu Buhari shine inganta hanyoyi, samar da tsaro, da kuma ruwansha da dai sauransu.

Ministan yace hanyoyi da suka hada da wanda ta tashi daga Adamawa zuwa Gombe yanzu haka ana cigaba da aikin gyran hanyar hakama na wanda ta had kananan hukumomin Mayo Belwa, Jada, Ganye da kuma Tongo itama aiki yayi nisa. Harma dana wasu jihohi dake fadin kasan nan.

A bangaren tsaro kuwa ministan yace gwamnatin tarayya tana iya kokarinta na ganin an kawo karshe matsalar tsaro da suka hada da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, fashi da makami, masu kai hare hare da sauransu.

A sahin wutan lantarkima sannu a hankali gwamnatin na kokarin ganin an magance matsalar baki daya musammanma a tashan wutan dake mambila a jahar Taraba.

Harwa yau ministan yace gwamnatin ta tarayar ta vimma nasarori da dama a bangarori dabam dabam da suka hada cin hanci da rashawa gyara layin dogo a wasu sassan kasan nan.

Don haka nema ya kirayi yan Najeriya da kasance masuyin adu o I a koda yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshn dukkanin kalubale da ke fuskantar kasan nan baki daya.

Exit mobile version