Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Sanannen Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yan jaridar da suke kiran yan bindiga da yan taadda ne asalin yan taaddan.
Kamar yadda Arise News ta ruwaito, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Arise ta yi da shi, ya ce akwai bu?atar a rungumi yan bindiga a alumma.
Daya daga cikin mai gabatar da shirin ya bayyana yadda hatsarin yan bindiga da yan taadda suke yayin da ya tambayi malamin abinda suke so kafin su zubar da makaman su.
A cewar Gumi, ya kamata a rungumi yan bindiga a alumma Yayin da Gumi yake amsa tambayar sa, ya ce ‘Yan jarida ne yan taaddan kuma bai dace su kira yan bindiga da yan taadda ba.
A cewarsa, yanzu haka a shirye yan bindiga suke da su zubar da makaman su, amma duk lokacin da su ka ji ana yada labarai akan su, ana kiran su da yan taadda, sai su hassala su ci gaba da gashi.
A cewar Gumi, matsawar ana so yan bindiga su daina addabar alumma su daina kashe-kashe, wajibi ne a rungume su a kyautata mu su kamar yadda ake yi wa sauran yan Najeriya.
A wani rahoton mai alaka da wannan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yan bindiga da ke adabar kasar nan suna kaunar wadanda ke girmama su tare da fahimtar halin da suke ciki.
Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga wurin dalibai a wurin makala da aka yi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a ranar Laraba. Malamin wanda ya dade yana ziyartar yan bindiga a daji don yunkurin yin sulhu da su ya ce bai samu wani matsala ba wurin gana wa da su domin a koyaushe ta ‘kofa ya ke bi’.

