Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) dake karamar hukumar zariya a arewacin jihar Kaduna ta fitar da sanarwan sace yan bindiga sun shiga jami’an inda su kayi garkuwa da babban malamin jami’ar da mai dakinsa da kuma diyar sa guda daya.
Daraktan sashen yada labarai na jamiar Ahmadu Bello Zaria Malam Auwalu Umar ya fitar da sanarwan a yammacin yau litinin inda ya bayyana cewa a safiyar yau Litinin da misalin karfe 12.50 na dare masu garkuwa da mutane suka shiga gidajen malaman jamiar ABU dake Samaru inda suka dauki wani maaikacin jamiar da matarsa da kuma yarsa.
Sai dai masu kula da tsaron jami’ar sunyi hanzarin sanar da jami’an yan sanda inda nan take suka bi sawun yan bindigar wanda hakan ya janyo musayar wuta tsakanin yan ta’addan da jami’an tsaro inda jami’an yan sanda suka samu nasarar kwato matar malamin da kuma yarsa a dai dai kauyen kasuwar Da’a dake bayan jami’ar ta ABU.
Sai dai kuma yan ta’addan sun samu nasarar gudu da malamin jami’an.
Jamiar ABU d ta ce tuni ta sanar da hukumomin tsaro lamarin, daga karshe hukar makarantar ta shawarci sauran mutanen jami’an da sauran makotan su dasu kwantar da hankalulan su.

